An gabatar da kasafin kudi na 4.3 tn a Nigeria

Image caption Gwamnati ta rage kudin gangan danyen man da ta yi niyya a kasasfin daga dala 78 zuwa 65 saboda faduwar farashi

Ministar kudi ta Nigeria, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta gabatar da kasafin kudin badi ga majalisar dokokin kasar, wadda aka yi hasashen kashe naira 4.3 tiriliyan.

A wani jawabi da ta yi ga manema labarai a Abuja bayan gabatar da kasasfin kudin, ministar ta ce a yanzu gwamnati ta kayyade kudin kowacce gangar danyen mai a kan dala 65 duk da faduwar farashin a kasuwannin duniya.

Ta ce "Mun bar kudin a haka ne saboda muna sa ran a shekara mai zuwa matsakaicin farashin da za a sayar da gangar danyen mai ba zai wuce dala 65 zuwa 70 ba."

Inda ta kara da cewa kasar na hako gangan danyen mai 2.2 miliyan a kullum, kana suna fatan cike gibin kasafin kudin daga kudaden shigar da za a samu daga wasu bangarori da ba na mai ba.

Ngozi ta kuma bayyana cewa sun rage bunkasar tattalin arzikin kasar daga kashi 6.35 cikin dari zuwa kashi biyar da digo biyar cikin dari.