An yanke wa sojin Nigeria hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wasu daga cikin masu gabatar da kara a gaban kotun ke nan

Wata kotun sojin Nigeria ta yanke hukuncin kisa akan wasu sojojin kasar 54 kan laifin bijirewa hukuma da kin zuwa yaki.

Kotun ta same su da laifin bijire wa hukuma da kin zuwa filin daga domin yaki da 'yan kungiyar Boko Haram a wasu garuruwa a arewa maso gabashin kasar.

Sojojin sun musunta tuhumar da aka yi musu.

Lauyan da ke kare su, ya ce an saki biyar daga cikin sojojin bayan an wanke su.

Tun a watan Oktoba aka fara shari'ar wadda aka yi a bayan idon jama'a.

Sojojin Najeriya da ke fada da 'yan Boko Haran na kokawa da rashin kayan aiki, kuma da yawa daga cikinsu rahotanni na cewa sun gudu.