Amurka da Cuba za su sake kulla hulda

Barack Obama da Raul Castro Hakkin mallakar hoto AFP Getty

Shugaban Amurka, Barrak Obama, da takwararsa na kasar Cuba, Raul Castro, sun sanar da cewa kasashe biyun za su fara tattaunawa don sake kulla huldar difilomasiyya nan da watanni kadan masu zuwa.

Shugaba Obama ya bayyana sabon shirinsa a kan dangantaka tsakanin Amurka da Cuba da cewa shi ne mafi muhimmanci a cikin sama da shekaru hamsin din da suka gabata.

A jiya Talata ne Shugabanni biyun suka tattauna da juna, inda suka amince a kan wasu matakai, ciki har da musayar fursunoni da kuma sassauta takunkumin tafiye-tafiye da kuma kasuwanci.

Kazalika Amurka ta ce za ta bude ofishin jakadancinta a Havana.

Shugaba Obama ya ce, “Da wadannan sauye-sauyen da nake sanarwa yau din nan, Amurkawa za su samu saukin zuwa Cuba, kuma za su iya amfani da katinsu wajen cirar kudi a bankunan kasar Cuba.”

Shi ma shugaban kasar Cuba, Raul Castro, ya bukaci Amurka da ta cire takunkumin cinikin da ta kakaba wa kasar tasa.