Amaechi ya zama shugaban kamfe na Buhari

Image caption Rotimi Amaechi ya yi fice wajen sukar shugaba Jonathan

Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, APC, ta nada gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben Janar Muhammadu Buhari.

Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinta, Alhaji Lai Mohammed ya aikewa kafafen watsa labarai.

Jam'iyyar ta kara da cewa ta yi imani Mr Amaechi yana da kwarewar tallata dan takarar shugabancin kasarta, kasancewarsa gogaggen dan siyasa.

Gwamnan na jihar Rivers dai ya yi fice wajen sukar shugaban kasar, Goodluck Jonathan, inda yake bayyana shi a matsayin mutumin da bai iya shugabanci ba.