Apple ba ya kula da ma'aikatansa

Hakkin mallakar hoto AFP

Shirin BBC Panorama ya bankado irin wahalhalun da ma'aikatan masana'atun kasar China dake samarwa da Apple kayayyaki suke fuskanta.

Wani bidiyo da aka dauka na aikin samar da wayar iPhone 6 ya nuna kamfanin Apple na karya alkawarinsa na kare ma'aikata.

An gano cewa ana saba ka'ida a lokutan da ya kamata ace ma'aikata su na dauka su na aiki da wajen katinan shaidar aiki da kuma wajen gudanar da taruka na aiki.

Sai dai kamfanin Apple ya ce bai amince da abubuwan da shirin na BBC ya bankado ba.

An dauki bidiyon ma'aikatan da suka galabaita su na bacci a aikin da suke yi na sa'oi 12 a masana'antar Pegatron dake wajen birnin Shanghai na kasar China.

Wani dan jarida da ke aiki cikin sirri, a wata masana'anta dake yin kayayyakin kwamfutar Apple na aiki kwanaki 18 a jere, duk da ya sha nuna bukatar ya na son ya huta na kwana daya kachal.

Wani dan jaridar har ila yau ya ce yana aiki sa'oi 16, ya ce kuma 'duk sanda na kwanta, bana son ko motsawa'.

'Ko da ace ina jin yunwa, ba zan iya mikewa na ci abinci ba, so nake kawai na kwanta na huta, bana iya bacci da daddare saboda gajiya' in ji shi.

Kamfanin Apple dai ya ki amincewa a yi hira da shi a shirin na BBC, amma a wata sanarwa ya ce ' Muna sane da cewa babu wani kamfani da yake yin abinda Apple yake yi domin tabbatar da cewa ma'aikata na aiki karkashin yanayi mai kyau'.

Apple ya kara da cewa abu ne da aka saba gani ma'aikaci ya dan runtsa a lokacin da yake hutawa, amma ya ce zai gudanar da bincike game da hujjar dake nuna cewa ma'aikatan na bacci a bakin aiki (saboda gajiya)