Sheriff ya musanta alaka da Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A baya wani dan kasar Australia ya yi zargin cewar Modu Sheriff yana da alaka da kungiyar Boko Haram

A Najeriya, yayin da ake fama da hare- haren mayakan kungiyar Boko Haram, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya musanta zarge- zargen cewa yana daga cikin masu daukar nauyin kungiyar.

Tsohon gwamnan jihar Bornon na maida martani ne dangane da gurfanar da wasu mutane shida da hukumar tsaron farin kaya wato SSS ta yi, bisa zargin su da kitsa makarkashiyar cewa su na cikin kwamandojin Boko Haram.... wadanda ke yunkurin sasantawa da gwamnatin Nigeria.

Ita dai hukumar ta SSS din ta yi ikirarin cewa mutanen da ta gurfanar sun amsa cewa su na da alaka da Dr. Stephen Davis, wani dan kasar Australiya mai tattaunawar neman sakin wasu da 'yan kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su.

A tattaunawar sa da BBC, Sanata Ali Modu Sheriff ya ce kalaman da wadanda aka gurfanar su ka yi, gaskiya ce ta yi halin ta.

Sanata Ali Sheriff ya kuma musanta zargin da wasu ke yi cewa a lokacin mulkinsa ne aka fara fuskantar rikicin 'yan Boko Haram ba, inda ya ce rikicin ya samo asali ne daga jihar Yobe a shekarar 1992, kuma ya ce a lokacin ba ya kan mulki.

'Gaskiyar magana shi ne Boko Haram ba ta soma a lokaci na ba' in ji Modu Sheriff