Boko Haram: An sace mata da yara 200 a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram na barna a Nigeria

Mayakan Boko Haram sun sace mata da kananan yara kusan 200 sannan kuma suka kashe mutane fiye da 30 a wani kauye a jihar Bornon Nigeria.

Mazauna kauyen Gumsuri da ke karamar hukumar Damboa, sun shaida wa BBC cewar an kai harin ne a ranar Lahadi kafin mayakan su tattara mata da kananan yara su wuce da su.

Sai dai wani dan kauyen Gumsuri wanda ya gudu zuwa Maiduguri, ya ce mutane fiye da 200 aka sace bayan sun bi gida-gida sun kirga yawan mutanen da ba a gani ba.

Kawo yanzu babu wata hanyar tantance adadin wadanda lamarin ya rutsa da su, saboda akwai yiwuwar wasu daga cikin mutanen sun fantsama cikin daji ne domin neman tsira.

Wani jami'in karamar hukuma ya ce "Mutanen sun tattara mata da kananan yara sannan suka tafi da su a cikin manyan motoci kafin su bankawa kauyen wuta."

Labarin harin na zuwa ne bayan kwanaki hudu saboda babu hanyoyin sadarwa a kauyukan jihar Borno.