An dambace a majalisar dokokin Kenya

Image caption An bai wa hammata iska a cikin zauren majalisar

'Yan adawa a majalisar dokokin kasar Kenya sun kawo tarnaki a mahawarar da majalisar ta fara kan wata sabuwar doka da ta shafi tsaro a kasar.

An dage zaman majalisar na wucin gadi, bayan da 'yan majalisar suka rika daka wa takwarorinsu tsawa a lokacin da suke magana, tare da yin wake na bore, da kuma jifa da takardu a kasa.

Lamarin daga baya ya kara rinchabewa, inda wasu 'yan majalisar suka shiga bai wa hammata iska.

Charles Keter, daya ne daga cikin 'yan majalisar dokokin Kenya karkashin jam'iyyar URP, ya ce "Ina mai matukar ba da hakuri kasancewana daya daga cikin 'yan majalisa, mun zubar da mutuncin mu inda wasunmu suka dambace, a maimakon mu bi ta hanyar da za ta fishe ma kasarmu."

An girke jami'an tsaro da yawa a kusa da ginin majalisar, bayan samun rahotannin da ke cewa jama'ar gari suna shirin gudanar da zanga-zanga.