INEC ta kafa kwamiti kan 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Zaben 2015 na cike da kalubale a Nigeria

Hukumar zaben Nigeria, INEC ta kafa wani kwamiti na musamman domin duba yadda wadanda suka rasa muhallansu a tashin hankali za su iya kada kuri'a a zaben 2015.

Shugaban INEC, Attahiru Jega wanda ya kafa kwamitin mai wakilai tara, zai soma aiki ne a ranar 26 ga watan Disambar 2014

Kwamitin na da alhakin yin nazari a kan yawan 'yan gudun hijirar da kuma yadda za a basu damar yin zabe a badi.

Kundin zaben Nigeria ya ce mutum zai kada kuri'a ne kadai a mazabarsa inda ya yi rajista.

Rikicin Boko Haram ya daidaita dubun dubatar mutane musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.