Isra'ila ta soma luguden wuta a zirin gaza

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin Isra'ila da Gaza ya janyo asarar rayukan jama'a a baya

Rahotanni daga Gabas ta Tsakiya na cewa wani jirgin yakin Isra'ila ya kai wasu hare hare ta sama a yakin Zirin Gaza.

Bayanai sun ce hare-haren Isra'ilan martani ne ga rokar da aka harba daga yankin na Gaza zuwa yankunan Yahudawa.

Wannan shine hari na farko da Isra'ila ta kai tun bayan kawo karshe samamen da ta kaddamar a yankin na Zirin Gaza a watan Agusta.

Mazauna yankin Gaza sun ce sun ji karar fashewar wasu abubuwa masu karfi har sau biyu.

Jami'ai sun ce ba a samu wadanda farmakin ya shafa ba.