'Cin gashin kan kananan hukumomi ya fuskanci cikas'

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption 'Yan majalisun dokokin Nigeria na yunkurin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima

Majalisun dokokin jihohin Nigeria sun yi fatali da batun bai wa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu a yukunrin da ake na yi wa kudin tsarin mulkin kasar kwaskarima.

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton da majalisun dokokin jihohin kasar suka mikawa majalisar dokokin tarayya ranar jumu'a a Abuja game da gyare- gyaren kundin tsarin mulkin kasar.

Su dai 'yan majalisar dokokin kasar na tarayya sun amince a bai wa kananan hukumomin 'yancin cin gashin kansu a mahawarar da suka tafka.

Kuma a cikin watan Oktoba ne dai majalisar dokokin ta tarayya ta aikewa majalisun jihohin kundin tsarin mulkin da aka yiwa gyaran fuska, domin su amince da gyare gyaren da ta yi.

Batun bai wa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu ya janyo zazzafarar mahawara a bakin 'yan kasar.