An soma amfani da sabuwar Naira 100

Hakkin mallakar hoto Nigeria State House
Image caption Darajar kudin Nigeria na ci gaba da faduwa

A Najeriya yanzu haka an soma amfani da sabuwar takardar kudi ta Naira 100 a hukumance wadda gwamnatin Nijeriyar ta bullo da ita.

Hukumomin kasar dai sun ce za a ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 100 da kuma sabuwar da aka samar a lokaci guda.

An kirkiro da sabuwar takardar kudin ta Naira 100 domin tunawa da cikar kasar shekaru 100 da kafuwa.

Hakazalika shigowar sabuwar takardar kudin na zuwa ne a daidai lokacin da darajar kudin Nigeriar ke ci gaba da faduwa sakamakon faduwar farashin mai a kasuwar duniya.