Gwamnati ta kaɗu a kan sace mutane 200 a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau ya ce za su ci gaba da kaddamar da hare-hare a Nigeria

Gwamnatin Nigeria ta ce ta yi "makutar kaduwa da kuma jin takaici" bayan da wasu mayaka suka kai hari a wani kauye suka kuma sace mutane kusan 200.

Ana zargin 'yan Boko Haram da wannan aika-aikar, ciki har da kashe mutane kusan 34 a kauyen Gumsiri na jihar Borno.

Wani babban jami'in gwamnatin Nigeria, Mike Omeri a wata sanarwa ya yi Allahwadai sannan kuma ya ce bukatar 'yan bindigar ita ce su saka tsoro a zukatan al'umma.

Tun a ranar Lahadi lamarin ya auku amma sai a ranar Alhamis aka ji labarin bayan wani mutumi da ya tsira ya kai Maiduguri sannan ya ba da labarin abin da ya auku.

Omeri ya ce "A wannan lokacin ba za a iya tantance adadin wadanda aka sace ba saboda wasu mutanen su fantsama cikin daji a lokacin hari."

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria tun daga shekara ta 2009.