Kutsen Sony: Za mu maida martani - Obama

Sony Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obama ya ce bai kamata kamfanin Sony ya soke kaddamar da shirin ba

Shugaban Amurka Barack Obama ya sha alwashin za su maida martani game da kutsen da ake zargin Koriya ta Arewa da aikatawa.

Obama ya kuma kara da cewa kamfanin Sony wanda kutsen ya shafa ya yikuskure da ya soke kaddamar da wani shiri da zai nuna yadda aka kashe shugaban kasar Koriya ta Arewa, wato Kim Jon-un.

A ranar juma'a ne hukumomin Amurkan suka danganta koriyar da kutsen wanda ya fitar da bayanai masu muhimmanci baina a jama'a.

Hakan ya sa kamfanin na Sony ya janye shirin bayan wannan barazana da ya samu.

" Za mu maida martani" Obama ya bayyanawa manema labarai a ranar juma'a ba tare da ya bayyana matakin da Amurkan za ta dauka ba.

Ya kuma kara da cewa "ba za mu amincewa wani dake waje ya dinga tace mana finafinanmu ba."

A cewar Mr. Obama ya na da matukar muhimmanci kundin adana bayanai na hukuma da ma na jama'a su kasance a tsare saboda muhimmancinsu akan tattalin arziki da rayuwar jama'a ta yau da kullum.

Ya kuma jaddada cewa kuskure ne da aka dage kaddamar da shirin fim din.

"Amurka ba za ta canza yanayiN rayuwarta ba saboda gudun harin 'yan ta'addanci."