Kutsen Sony: Mai Snapchat ya nuna takaicinsa

Sony
Image caption Evan Speigel ya nuna takaicinsa kan wannan lamar

Mutumin da ya kirkiro da fasahar aikewa da sako ta Snapchat ya nuna takaicinsa da fushi bayan da aka fallasa wasu bayanansa.

Bayanan na Evans Spiegel sun fita baina jama'a ne bayan kutsen da aka yi akan kamfanin Sony.

Spiegel ya dai aikewa da Michael Lyton, shugaban gudanarwa na Sony, wasu daga cikin tsare-tsarensa na ta kafar email.

Daga cikin bayanan da aka sata a cewar Mr. Spiegel har da bayanan akan kudaden da aka sayo wasu kayayyaki.

"Na ji kamar na yi ta kuka a duk safiya." Mr Spiegel ya fada a wata wasika da ya rubuta.

Ya kara da cewa "sai na tafi na dan yi tattaki inda na yi tunani akan wasu abubuwa da dama."

Bayanan da aka sata har ila yau sun hada da wata fasaha da za ta baiwa masu amfani da Snapchat damar aikewa da sakonni da hotunan bidiyo.

Kamar yadda sakon email ya nuna, kamfanin na Snapchat ya sayo wata na'ura ta ido da za ta samar da wata na'ura makamancin irin ta Google Glass.