'Ba za a iya murkushe mayakan IS yanzu ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana ci gaba da fafatawa da mayakan IS

Babban kwamandan kasar Amurka dake jagorantar sojin kasar a yakin da ake yi da 'yan kungiyar ta IS ya ce sai an kwashe akalla shekaru uku ana yakar 'yan kungiyar kafin a samu galaba a kansu.

A cewar Laftanar Janar James Terry, harin saman da Amurka ta kai na farko ya fara ne watanni hudu da suka gabata, kuma ana bukatar a kara nuna hakuri.

Yayin da yake ikirarin cewa dakarun Kurdawan dake samun goyon bayan takwarorinsu na Amurka, su na samun nasara.

Kakakin Ma'aikatar tsaron tsaron Amurka, ya ce a hare-haren da ake kaiwa na hadin gwiwa, an kashe manyan mayakan kungiyar ta IS da dama a cikin watan da ya gabata, lamarin da a cewrasa ya gurgunta ayyukan kungiyar.