An kashe 'yan Boko Haram sama da 100 a Borno

Hadin gwiwar sojoji da 'yan kato da gora Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hadin gwiwar sojoji da 'yan kato da gora

A Najeriya, jama'ar Dambua dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar sun ce sojoji da mutanen gari sun kashe kimanin 'yan kungiyar Boko Haram 115 a ranar Juma'a.

Wasu mazauna garin suka ce maharan sun isa garin ne lokacin da ake shirin gudanar da sallar Juma'a, inda suka firgitar da jama'a da harbe-harbe.

Harin ya zo ne kasa da mako daya da wasu maharan suka kashe mutane 33 da sace wasu 200 a Gumsuri dake cikin karamar hukumar ta Dambua.

Karo na uku kenan da 'yan kungiyar Boko Haram ke kokarin kai hari garin na Dambua tun bayan da sojoji suka kwato garin daga hannanun 'yan kungiyar a cikin watan Satumba, bayan wata daya yana hannunsu.

A wani labarin kuma, rahotannin sun ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kashe jami'in dan sanda guda lokacin wani hari ranar Juma'a a kauyen Damagun, dake karamar hukumar Fune a jihar Yobe.