An yi jana'izar dan sandan Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty

Dubban Mutane na halartar jana'izar daya daga cikin 'yan sandan da aka kashe a Amurka, a makon jiya.Mutanen da sun hada da 'yan sanda taru a birnin New York inda aka yi addu'o'i a coci.

Magajin Birnin New York Bill de Blasio ya ce "New York ta rasa gwarzo, kuma hazikin mutum saboda sadaukar da kai da yayi wajen nuna kara ga duk wadanda ya yi mu'amala dasu.

Mataimakin Shugaban kasar, Jo Baiden ya shaida wa jama'a cewa kisan dan sandan da abokin aikin sa ta jijjiga kasar baki daya.

A makon jiya ne wani bakar fata ya hallaka 'yan sandan biyu lokacin da suke cikin motar su ta sintiri a birnin.

A farkon wannan watan, bakaken fata dadama sun yi ta zanga-zanga a kasar saboda kisan bakake da ake zargin 'yan sanda ke yi.