Za mu maida martani ga Korea - Obama

Sony Hacking Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama ya ce kuskure ne soke fitar da fim din da kamfanin Sony ya yi

Shugaba Barack Obama ya ce Amurka za ta maida martani ga Korea ta Arewa, saboda satar bayanai da ta yi a kamfanin Sony pictures mai shirya fina-finai.

Mr Obama ya kara da cewa ba za su zura ido suna kallo masu mulkin-kama karya suna yi musu shishshigi a harkokinsu ba.

Ya kuma ce martanin da Amurkan za ta mayar zai kasance daidai da abinda Korea ta aikata.

Har ila yau Obama ya ce kamfanin Sony Pictures ya yi kuskuren soke fitar da fim da yake yin shagube ga shugaban Korea ta arewan Kim jong Un.

Sai dai kamfanin ya kare kansa inda ya ce wannan matakin da ya dauka ya zama dole domin manyan gidajen sinima da dama a Amurka sun ce ba za su nuna fim din ba.