"Akwai karancin ilimin amfani da nau'rar cutar Asma"

Asthma
Image caption Rashin iya amfani da na'urar kan iya halaka masu fama da cutar

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa mafi yawan masu fama da cutar Asma ba sa amfani da na'urar dakile cutar yadda ya kamata a lokacin gaggawa.

Binciken wanda wata cibiya mai suna UK Asthma ta gudanar, ya nuna cewa ba a koyawa masu fama da cutar ta daukewar numfashi yadda ake amfani da na'urar.

A kuma cewar wata cibiya mai suna Allergy UK, masu cutar sukan shiga rudani idan sun tashi amfani da ita.

Binciken har ila yau ya nuna cewa kashi bakwai cikin mutane dari ne kawai suke amfani da na'urar ta yadda ya kamata.

Hakan ya sa cibiyoyin suka yi kira da a kara inganta horan da ake baiwa masu fama da cutar sannan a kara ilimantar da ma'aikatan kiwon lafiya.

Daga cikin matsalolin da akan fuskanta a wajen amfani da na'urar ta cutar Asma akwai yadda ake kuskuren rike na'urar na tsawon dakikoki 10 tare da gazawa wajen danna ta da karfi.

Haka kuma an gano cewa akwai wasu lokuta da masu cutar kan manta da umurnin yin amfani da na'urar koda an koya musu.

Wannan kira na zuwa ne bayan da wani bincike da aka gudanar a Amurka ya nuna cewa kashi 16 cikin dari ne kawai suke amfani da matakan kare lafiya daidai a lokacin da rayuwarsu ta shiga wani mayuwancin hali.