Guinea: Matasa sun fatattaki ma'aikatan Ebola

Hakkin mallakar hoto Getty

Rahotanni na cewa matasa sun gudanar da zanga zanga a Guinea inda suka hana ma'aikatan kiwon lafiya kafa wata cabiyar kula da masu fama da cutar ta Ebola a Kudancin kasar.

'Yan sanda sun ce masu zanga zangar sun kona tantuna da dama, sun kuma fatattaki ma'aikatan kiwon lafiya dake yankin.

Rahotanni daga Laberiya kuma na cewa an samu karancin mutane a wajen kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dattawan kasar da aka gudanar.

Sau biyu dai hukumomin kasar suke dage zaben, saboda barkewa cutar Ebola, lamarin da ake ganin ya yi tasiri wajen kin bayyanar mutane a rumfunan zaben.

Yayin gudanar da zaben, rahotanni sun ce an umurci masu kada kuri'a da su tsaya da tazarar mita daya a tsakaninsu, sannan an kuma dauki yanayin zafin jikinsu a lokacin zaben.