Obama ya yi tir da kashe 'yan sanda

'Yan sandan da ake kashe a New York Hakkin mallakar hoto EPA

Shugaban Amurka Barrack Obama ya yi Allah wadai da kisan wasu 'yan sanda biyu da aka yi birnin New York.

Obama, wanda yake hutu a Hawaii ya ce: "'Yan sanda sun sadaukar da rayuwar su wajen kare mu, don haka yakamata mu girmama su mu kuma gode musu a koda yaushe."

Kwamishinanan 'yan sandan birnin ya ce an kashe su ne kawai saboda suna 'yan sanda.

Jami'an kasar sun ce wani bakar fata ne yayi kisan, mai suna Ismaaiyl Brinsley, mai shekaru 28.

Mutumin ya kuma bayyana aniyar sa ta kashe 'yan sanda ta internet, inda ya ce zai dauki fansa akan 'yan sanda saboda kisan da suka yi wa Erick Garner, wani dan bakar fata.

Mutumin ya kuma kashe kansa bayan harbe 'yan sandan.

Bill de Blasio, magajin birnin New York ya ce: "muna zaman makoki a birnin mu; cike muke da alhini. Mun rasa mutane biyu na gari, da suka sadaukar da rayuwar su wajen kare mu.