Bam ya hallaka mutane 7 a Bauchi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kimanin mutane 25 sun jikkata sakamakon fashewar bam a kasuwar Bauchi

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 7 sakamakon fashewar bam a babbar kasuwar birnin jihar a ranar Litinin.

Kakakin rundunar, DSP Haruna Mohammed ya ce kimanin mutane 25 ne suka jikkata sakamakon al'amarin wanda ya auku da yamma.

Harin na Bauchi ya auku ne sa'o'i kadan bayan wanda aka kai harin a birnin Gombe mai makwabtaka da ita, inda mutane sama da ashirin suka mutu, sakamakon fashewar wasu tagwayen bamabamai a tashar mota.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare haren, amma sun yi kama da wadanda yan Kungiyar Boko Haram ke kaiwa a sassa daban daban na arewacin Nijeriya.