BBC ta gano masu laifi a internet

Internet Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yaudari matashin mai shekaru 17 ta hanyar amfani da internet.

BBC ta gano wasu 'yan asalin kasar Philippine da ake zargin sun yaudari wani matashi dan Birtaniya a shafin Internet da ya kashe kansa.

Matashin mai suna Daniel Perry mazunin yankin Dunfermline mai shekaru 17, ya rasa ransa ne a lokacin da ya fado daga gadar Fourth Bridge a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Wasu ne dai suka yaudare shi, ka na sukai lalata da shi ta hanyar amfani da Internet, mutanen kuma mazauna kasar Philippines ne, haka kuma bai gano su ba har sai lokacin da suke hirar hoton bidiyo wato Skype a turance.

Wadannan mutane dai sun nadi hoton bidiyon Daniel, inda daga bisani suka fara yi masa barazanar za su wallafa shi a shafin internet indai bai ba su kudi ba.

Binciken da BBC ta yi ya gano cewar an yi ta aikewa Daniel sakon wayar salula ana cewa ''Sai mun tagayyara ka''.

Lamarin da ya sa ya yi fushin zuciya tare da fadowa daga gadar Fourth Bridge, kuma nan take ya rasa ransa.

A lokacin da BBC ta kalubalanci mutanen biyu, sai suka musanta su na da hannu kan lamarin.

Mutane biyun daga cikin ukun da ake tuhuma, wadanda aka cafke su a babban birnin kasar Philippines wato Manila a wannan shekarar, sai dai suma kamar dayan mutumin da ake tuhuma an bada su beli.

Shi dai Daniel a zatonsa da mace ya ke hira ta Internet, wadda yake tunanin shekarunsu za su zo daya.

Kungiyoyin masu aikata muggan laifuka na amfani da matasa ta shafin Internet su yi lalata da su, inda sukan danawa manyan mutane tarko ta yin amfani da hoton zukekiyar budurwa domin su ja hankalinsu.