Beji Caid Essebsi ya lashe zaben Tunisia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Beji Caid Essebsi zai kasance shugaban farko na dimokaradiyya

Hukumar zaben Tunisia ta ayyana Beji Caid Essebsi a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar.

Hukumar zaben ta ce Essebsi ya lashe zaben da fiye da kashi 55 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Shi ne ke zama shugaban kasa na farko da aka zaba a turbar dimokaradiyya a kasar.

A kasar ta Tunisia ne dai aka fara boren da ya yi sanadiyar juyin juya hali a kasashen larabawa.