Ribar Kamfanin Blackberry ta ragu

Hakkin mallakar hoto

Kamfanin wayar salula ta Blackberry ya bayar da rahotan komabaya a ribar da kamfanin yake samu

Ribar Blackberry ta fadi zuwa $793 daga $ 1.19 a bana

Babban jami'in kamfanin Blackberry John Chen ya ce alkaluman ribar kamfanin basu gamsar ba

Sai dai ya kara da cewa kodayake Blackberry zai iya murmurewa a nan gaba, sannan ribarsa ta karu zuwa shekarar 2016 amma sai dai ba zai iya yin alkawarin cewa za a samu riba ba

Hannayen jarin kamfanin ya fadi da fiye da kashi 6% bayan an fitar da alkaluman komabaya a ribar amma daga bisani hannayen jarin sun hau