CAR: Musulmi na cikin mummuna hali

Image caption 'Yan kungiyoyin kiristoci na cin zarafin musulmai a kasar

Rahotanni daga Jamhuriyar Tsakiyar Afrika na cewa akwai daruruwan Musulmi da ke zaune a yammacin kasar cikin wani mummunan yanayi na kuncin rayuwa.

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Human Rights Watch ta ce mutanen na fargabar barin sansanonin da suke domin gudun kada a kai masu farmaki.

Rahoton ya ci gaba da cewa su kan su jami'an Majalisar Dinkin Duniya da kuma gwamnatin rikon kwaryar kasar sun hana wadannan mutane barin wadannan wurare su nemi mafaka a kasashen waje.

Hakan na faruwa ne duk da cewa ba a ba su wata kariya ba daga hare hare da ake zargin kungiyar 'yan banga ta Kiristoci ta anti-Balaka ke kai wa a kan su.