FIFA ta tattauna kan makomar Blatter

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blatter zai nemi shugabancin Fifa ne karo na biyar a jere

BBC ta fahimci cewa an yi ganawar sirri tsakanin jami'an Fifa da shugabanta, Sepp Blatter domin tattauna wa kan makomarsa a matsayinsa na shugaban hukumar.

Ganawar da jami'an suka yi ta kunshi jami'an hukumomin kwallon kafa na kasashe da dama, kuma an fara yin tattaunawar ce tun a wata Oktoban 2013, lokacin bikin cikar hukumar shekaru 150 da kafuwa.

Tuni da Blatter ya tabbatar cewa zai kara neman shugabancin hukumar a watan Mayu mai zuwa, kuma idan ya yi hakan, to zai zama shugaban hukumar sau biyar a jere.

Sai dai jam'ain hukumar na ci gaba da nuna damuwa ganin cewa ranar da aka ware domin cikar wa'adi ga duk wanda ke sion yi takarar shugabancin hukumar ya yi hakan kafin 29 ga wata Janairu na karatowa.

A lokacin da Blatter ke yin jawabi a Manilla a farkon watan nan, ya bayyana cewa ya samu goyon bayan hukumomin kwallon kafa na nahiyoyi shidan da suka kafa hukumar ta Fifa.