Yawaitar hare-hare a Faransa

Shugaban Faransa Francois Hollande Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Hollande yace kad al'umar Faransa su kadu d hare-hren.

Shugaba Francois Hollande ya bukaci al'umar kasar Faransa da kada su damu sakamakon hare-hare uku da aka kaiwa jami'an 'yan sanda da kuma mutanen gari a 'yan kwanakin nan.

Mr Hollande na magana ne bayan wani mutum a cikin mota ya afkawa dandazon mutane da ke sayayyar kirsimati a wata kasuwa da ke yammacin birnin Nantes, da ya jiwa mutane 10 rauni.

Masu shigar da kara harin ya yi kama da wanda aka kai a yankin Dijon a ranar lahadi, inda wani direba da ya ke ihu tare da ambato wasu kalmomin addinin musulunci ya afkawa wasu mutane a wani babban shagon saida kayayyaki da ke yankin.

Har wayau a ranar asabar ma an harbe wani mutum, bayan ya dabawa jami'in dan sanda wuka a kusa da tsakiyar birnin Tours.