Mayakan IS na lalata da matan Yazidi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayakan IS sun kama garuruwa da dama a Iraki da Syria

Ana kara samun bayanai kan irin cin zarafin da 'yan ta'adda a Iraki ke yi wa matan da suke kamewa su kuma sai da su a matsayin bayi da ake lalata da su.

Wadanda abin ya rutsa dasu 'yan kabilar Yazidi su ka kuma samu tserewa sun shaidawa BBC irin abubuwan tashin hankalin da suka fuskanta a hannun 'yan ta'addar na IS.

Sun yi magana kan kasuwar bayin da ake saida manya da yaran mata a kan farashin dala goma sha biyu kacal.

Ana kuma sa ke maida wasu da suka tsere tun farko bayan an musu duka an ji mu su rauni a kuma sake saidasu.

Wata cikin wadanda suka samu tserewa ta fadi yadda suke wulakanta a hannun 'yan ta'addar.

Ta ce ''Sun fito damu domin su sayar damu, mayaka da dama sun zo domin su saye mu, mu yi ta kuka muna ta rokon su amma ko a jikinsu.''

A wata takarda da ta fito daga hannun IS ta bai wa maharan dama da su maida duk wata mace 'yar kabilar Yazidi ko kuma kirista baiwa. Ta kuma ba su damar yin lalata da yara mata.