Jonathan ya roki 'yan PDP kada su fice

Image caption Rahotanni na cewa 'yan PDPn da suka fusata na yunkurin ficewa daga cikinta.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya roki 'yan jam'iyyarsu ta PDP da ba su kai gaci ba a zabukan fitar da gwani da kada su fice daga jam'iyyar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja, lokacin da 'yan jam'iyyar ke tara masa kudi domin yakin neman zabensa a shekarar 2015.

Jiga-jigan jam'iyyar da dama ne dai suka harzuka bayan zaben fitar da gwanin bai yi musu dadi ba.

Wasu daga cikinsu ma tuni suka fice daga jam'iyyar, cikinsu har da dan takarar gwamnan jihar Oyo, Alao Akala.

Kazalika wadanda suka harzuka sun hada da tsohon ministan watsa labarai, Labaran Maku da tsohon karamin ministan tsaro, Musiliu Obanikoro da mataimakin gwamnan Sokoto, Muktari Shagari.

Rahotanni dai na cewa wasu daga cikinsu na yunkurin sauya sheka daga jam'iyyar ta PDP zuwa wasu jam'iyyu domin yin takarar.

Shugaba Jonathan ya ce yana da masaniyar cewa da dama daga cikinsu ba su ji dadin abin da ya auku lokacin zabukan fitar da gwanin ba, yana mai cewa duk da haka bai kamata su fice daga jam'iiyar ba.

A cewarsa, zamansu a jam'iyyar ne kadai zai nuna cewa za su iya sadaukar da jin dadinsu domin tabbatar da mulkin dimokaradiyya.