Jihar Lagos ta taso keyar mabarata

Gwamnan jihar Lagos Babatunde Fashola Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin jihar Lagos kamr takwararta ta jihar Kano ta haramta yin barace-barace a duk fadin jihar.

Sama da mutane 70 ne aka iza keyar su daga jihar Lagos dake kudancin Nigeria zuwa jihar Kano, bayan sun shafe watanni a tsare a Lagos din, sakamakon kama su da aka yi suna bara.

Mutanen dai sun ce sun sha bakar wahala a yayin da suke tsare, abin da a cewar su ya sa wasun su suka ringa mutuwa.

Ita dai gwamnatin jihar Lagos din ta haramta barace barace a jihar, to sai dai wasu masu karamin karfi na yin biris da haramcin, inda suke yin barace barace a jihar ta Lagos duk da haramcin.

A cikin mabaratan da aka kama har da wani karamin yaro da yayansa ya gudu ya bar shi a lokacin da aka cafke su.

Ba dai 'yan asalin jihar Kano kadai hukumomin jihar Lagos suka danke ba, har da 'yan jihohin Niger, da Kebbi, da Jigawa, da Kaduna, da Sokoto, da Zanfara da kuma katsina.

Har wayau har da wani dan asalin kasar Ghana da kuma Jamhuriyar Nijar.