An soki PDP saboda tarawa Jonathan kudi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jam'iyyun da kujngiyoyin sun ce abin takaici ne kudin da aka tarawa Jonathan duk da yake 'yan kasar na cikin mummunan hali.

A Najeriya, kungiyoyi da jam'iyyu da dama sun soki jam'iiyar PDP saboda tarawa Goodluck Jonathan kudin yakin neman zabe lokacin 'yan kasar na cikin bakin talauci.

Jam'iyyar APC reshen jihar Lagos, ta bakin kakakinta Mr Joe Igbokwe ta ce PDP ta gaza kawo ci gaba a kasar amma ta tarawa shugaban kasa Mr Jonathan fiye da N21bn domin yin yakin neman zaben.

Kungiyar The Buhari Support Organizations, BSO da Human Right Writters Association of Nigeria suna cikin wadanda suka soki mutanen da suka tarawa Mr Jonathan kudin.

BSO ta ce abin mamaki shi ne cikin wadanda suka tara kudin har da hukumar samar da hasken wutar lantarki, wacce ta gaza sawarwa 'yan kasar hasken wutar lantarki.

Ita kuma Human Right Writters Association of Nigeria cewa ta yi ya kamata a yi amfani da kudin domin magance matsalolin rashin tsaro da suka addabi Najeriya.