Tunisia: Essebsi ya yi ikirarin nasara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu ba a bayyana sakamakon zaben Tunisia ba a hukumance

Rahotanni daga Tunisia na cewa dan takarar shugabancin kasar Beji Caid Essebsi ya yi ikrarin cewa shi ya lashe zaben da aka gudanar.

Essebsi ya samu sama da kashi 55 na kuri'un da aka kada yayin da ake ci gaba da kidaya.

A wani dan takaitaccen jawabi da ya yiwa magoaya bayansa da suka taru a kofar shelkwatar ofishinsa na yakin neman zabe, Mr Essebsi ya yi kira ga 'yan kasar da su hada kansu.

Sai dai abokin hamayyarsa, Moncef Marzouki ya ce Essebsi ya yi riga malam masallaci wajen cewa shi ya yi nasara.

Nan gaba ne dai ake saran bayyana sakamakon zaben.