Kirsimeti: Za a takaita zirga-zirga a Borno

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rundunar Sojin kasar ta ce ta samu bayanan sirri akan yiwuwar kai hare hare lokacin Kirsimeti

Hukumomin tsaro a jihar Borno da ke arewacin Nigeria sun ba da sanarwar takaita zirga zirgar ababen hawa a jihar.

Rudunar soji a jihar ta Borno ta ce za a takaita zirga zirga a duk fadin jihar tun daga ranar Laraba 24 ga watan Disamba har zuwa ranar Lahadi 28 ga watan.

Rundunar ta ce ta dauki matakin ne sakamakon bayanan da ta samu cewa 'yan kungiyar Boko Haram suna shirin kai hare-hare a garin lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Kazalika rundunar ta bukaci jama'a da su sa ido sosai, sannan su kai rahoton duk mutumin da ba su gane take-takensa ba ga hukumomin tsaro.

Wannan mataki ya zo ne a lokacin da rundunar 'yan sandan kasar ta ce zata karfafa matakan tsaro a dukkanin fadin kasar domin bukukuwan kirsimeti.