Chibok: "Jonathan ba shi da gaskiya"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyayen 'yan matan Chibok sun ce ba za su ji dadin kirismeti ba

Iyayen 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace fiye da kwanaki 250 da suka wuce sun ce shugaban Najeriya ba shi da gaskiya shi ya sa bai ba da muhimmanci wajen ceto 'yan matan ba.

Iyayen sun bayyana takaicinsu game da yadda 'yan matan ke ci gaba da kasancewa a hannun 'yan Boko Haram duk da yake bikin kirsimeti ya matso.

Daya daga cikin iyayen, ya shaidawa BBC cewa a bara warhaka 'yarsa wadda aka sace ce ke yi musu girke-girke da shirye-shiryen bukukuwan na kirsimeti, yana mai cewa duk lokacin da ya tuna cewa za a yi kirsimetin bana ba tare da ita ba hankalinsa yana matukar tashi.

A cewarsa, tun bayan ganawar da suka yi da shugaba Jonathan da alkawuran da ya yi musu na sako 'ya'yansu ba su kara jin komai daga gare shi ba.

Ya kara da cewa Mr Jonathan ya mayar da batun sace 'yan matan siyasa shi ya sa bai ba shi muhimmanci ba.

Ya roki 'yan Boko Haram su saki 'ya'yan nasu, yana mai cewa "mu talakawa ne bai kamata a sace 'ya'yanmu ba".

Batun sace 'yan matan Chibok din dai ya jawo kakkausar suka kan shugaba Jonathan, wanda tun da farko bai amince cewa an sace 'yan matan ba.