An hallaka mutane 27 a Gombe da Bauchi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram na hallaka jama'a

Mutane akalla 27 ne suka rasu sakamakon hare-haren da aka kai a jihohi biyu da ke arewa maso gabashin Nigeria a ranar Litinin.

Bam na farko ya fashe ne a wata tashar mota da ke Gombe inda mutane 20 suka rasu sannan na biyun kuma ya tashi a babbar kasuwar Bauchi inda a nan kuma mutane 7 suka rasu.

Wani jami'in kungiyar agaji ta Red Cross a Gombe, Abubakar Adamu Gombe ya ce mutane 40 ne suka samu raunuka sakamakon harin bam din da aka kai a tashar mota ta Dukku a Gombe.

Shi kuwa kakakin rundunar jihar Bauchi, DSP Haruna Mohammed ya shaidawa BBC cewa kimanin mutane 25 ne suka jikkata sakamakon lamarin.

Ana zargin kungiyar Boko Haram wadda ke da'awar yin jihadi da kaddamar da wadannan hare-hare.

Karin bayani