Intanet ta dauke sau biyu a Korea ta Arewa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sau biyu intanet na daukewa a Korea ta Arewa

Kasar Korea ta Arewa ta fuskanci matsalar daukewar intanet karo na biyu, acewar kamfanin gwada karfin intanet na Dyn Research.

A shafinsa na Twitter, kamfanin ya ce an samu daukewar intanet karo na biyu a ranar Talata da rana, sannan ya dawo bayan akalla sa'a daya.

Kamfanin ya ce "intanet na kasar Korea ta Arewa ya sake daukewa da misalin karfe 15.41 agogon UTC. Wannan ce daukewa ta biyu bayan intanet din ya dawo a daren Litinin".

Har yanzu dai babu abinda hukumomi suka ce dangane da lamarin.

An yi ta baza jita-jita akan ko wanene ke da alhakin daukewar intanet din, bayan rashin jituwar da aka samu tsakanin Korea ta Arewa da Amurka a kan harin kutse.

Kasar China ta musanta rahotanni da ke nuna ita ce keda alhakin daukewar intanet din.

Jami'an Amurka basu ce uffan ba a game da yiwuwar ko Amurka nada hannu a daukewar intanet din a Korea.

A baya dai Amurka ta ce zata dauki matakin daya dace sakamakon kutsen da aka yi wa kamfanin shirya fina-finai na Sony, bayan hukumar FBI ta ce Korea ta Arewa ce ke da alhakin kutsen.

Kutsen da aka yi wa kamfanin na Sony ya sa ya dakatar da nuna wani fim mai suna "The Interview" wanda a ciki, aka nuna yadda aka kashe shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un.