An kashe mutane 13 a Taraba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kai harin ne lokacin mutanen suna walimar daurin aure.

Rahotanni daga jihar Taraba da ke arewacin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun kashe mutane akalla 13 bayan sun bude musu wuta lokacin suna walimar daurin aure.

Rahotannin sun ce akalla mutane 30 ne suka samu raunuka lokacin da aka kai harin ranar Litinin da daddare a kauyen Nafirde da ke karamar hukumar Gassol .

Ana ganin harin ba shi da nasaba da hare-haren da Boko Haram ke kai wa, ganin cewa jihar ta Taraba na fama da kashe-kashen da ke da alaka da addini da kabilanci.

Mazauna kauyen sun dora alhakin harin kan kabilar Jukun, kodayake har yanzu kabilar ba su ce uffan ba.