Guguwa ta afkawa Amurka

Guguwa a Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ba wanann ne karon farko da ake samun guguwa mai karfin gaske a sassan Amurka ba.

Mahaukaciyar guguwa ta hallaka mutane 4 da kuma yin mummunar barna ta hanyar lalata gidaje da wuraren kasuwanci a jihar Mississippi ta kasar Amurka.

Dubban mutane na zaune babu wutar lantarki a gidajensu, abinda ya tilastwa gwamnan jihar Phil Bryant ya ayyana dokar ta baci.

Ya yin da a wata gundumar da ke jihar aka sake samun wata mummunar guguwa mai karfin gaske. Masu hasashen yanayi sun yi gargadin ta yi wu a sake samun guguwa a kudancin Amurka da suka hada da Louisiana, da Alabama da kuma Georgia.us_storm