Mayakan IS sun harbo jirgi a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar IS ce ke da iko da birnin Raqqa

Mayakan kungiyar IS a Syria sun harbo wani jirgin yaki mallakar kasashen kawance da Amurka ke jagoranta.

Wata kungiyar kare hakkin bil-adama ta Syria da ke da cibiyarta a London, ta ce an harbo jirginne a kusa da birnin Raqqa da ke karkashin ikon kungiyar IS.

Kungiyar ta ce an kama matuka jirgin wadanda Larabawa.

Babu bayanai kan yanayin da jirgin ke ciki.

Wasu rahotanni sun nuna cewar matuka jirgin 'yan kasar Jordan.

Kasar Jordan na cikin kasashen Larabawa da ke yaki da kungiyar IS.