Sojojin Nigeria 13 za su sha dauri a kurkuku

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Nigeria na shan suka kan yaki da Boko Haram

Wata kotun musamman ta sojin Nigeria ta yanke hukuncin daurin shekara bibbiyu ga wasu sojoji goma sha uku, wadanda aka kama da laifin guje wa fagen fama.

Sojojin an same su da laifin gudu lokacin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai harin kan makarantar Sakandaren Chiboka jihar Borno, inda suka sace mata sama da 200.

Kazalika kotun ta kama su da laifin yin sakacin da ya yi sanadin sace motar sintirin sojojin, kana ta sake yanke musu hukuncin daurin shekara biyu kowannensu.

Sai dai kotun ta ce za a yi musu horon hukunce-hukunce biyun ne lokaci guda, wato cikin shekara biyu.

Amma Lauyan da ke kare sojoji, Barrister Awwal Abdullahi ya shaida wa BBC cewa za su daukaka kara saboda ba su gamsu da hukuncin ba.

A cikin watan Afrilu ne 'yan Boko Haram suka sace dalibai 'yan makaranta fiye da 200 wadanda har yanzu gwamnati ta kasa ceto su.