Al-Shabab ta kai hari a sansanin AU

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al-Shabab ta dauki alhakin kai wannan harin

'Yan bindiga a kasar Somalia sun kai hari a babban ofishin dakarun samar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika AU wanda ke Mogadishu.

Kungiyar AU ta ce an kashe sojoji uku sannan an raunata a wani farar hula daya a lokacin da mayakan al-Shabab suka kutsa cikin sansanin wanda ke kusa da babban filin jirgin saman kasar.

Kungiyar ta ce an hallaka maharan da dama.

Bayan shafe fiye da sa'o'i biyu ana barin wuta, kungiyar AU ta sanarda cewa a yanzu kura ta lafa.

A cikin sansanin na Mogadishu, a nan ne Biritaniya da Italiya ke da ofisoshin jakadancinsu.