Ebola: An kafa dokar hana fita a Saliyo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar Ebola na cigaba da yaduwa kamar wutar daji

Gwamnatin kasar Saliyo ta kafa dokar hana zirga-zirga a arewacin kasar na kwanaki 3 domin magance matsalar cutar Ebola a yankin.

Mai magana da yawun gwamanti yace za a rufe kasuwanni da shaguna, kuma babu wata mota in dai ba ta gwamnati ba da za a bari ta kai-komo a titunan kasar.

Haka kuma an haramta duk wasu abubuwa da suka shafi taruwar jama'a ciki har da na addini, sai dai a yau ne kadai aka bar mabiya addinin kirista su yi shagalin kirsimati.

Kasar Saliyo na daga cikin kasashen da cutar Ebola ta fi kamari a Yammancin Afurka, inda aka samu fiye da mutane dubu tara da suka kamu da cutar, haka kuma hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewe cutar na kara yaduwa kamar wutar daji.