Iyaye sun ba da 'yarsu ga Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yarinyar ta ce iyayenta ne suka jefa ta a Boko Haram

Wata yarinya a Nigeria 'yar shekaru 13 ta bayyana yadda iyayenta suka mika ta hannun mayakan Boko Haram domin a yi amfani da ita a matsayin 'yar kunar bakin wake.

Yarinya ta bayyana wa taron manema labarai a Kano da 'yan sanda suka shirya cewar, an kawo ta Kano ne tare da wasu 'yan mata biyu domin su tayar da bam.

'Yan sanda sun ce sun damke yarinyar ce a ranar 10 ga watan Disamba sanye da abubuwa masu fashewa a jikinta.

A cewar yarinyar wasu shugabannin Boko Haram sun tambayeta ko ta san menene kunar bakin wake, sai ta ce musu ba ta sani ba.

Jami'an tsaro sun ce sun yi nasarar dakatar da ire-iren wadannan 'yan kunar bakin wake a wasu yankuna na arewacin kasar.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wani ikirarin da yarinya ta yi a gaban jami'an tsaro.