"A daina gallazawa kananan kabilu a Syria"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kirismeti na biyu da Paparoma ya jagoranta

A sakonsa na bikin Kirsimeti, Paparoma Francis ya yi Allah wadai da yadda ake gallazawa kananan kabilu a kasashen Syria da Iraki.

Dubun dubatar jama'a ne suka hallara a dandalin St Peter's Square a birnin Rome, don sauraron Paparomar na jawabin isar da sakonni da sa albarka--a bikin Kirisimetinsa na biyu tun bayan da aka zabe shi a bara.

Paparoman ya yi nuni da halin da wadanda yaki ya daidaita, musamman a kasashen Syria da Iraki da cewa.

Ya ce ''Ina roko ga mahaliccin duniya, da ya duba halin da yannuwanmu suke ciki a kasashen Syria da Iraqi da suka dade suna fama da bala'in da yakin da ake yi ya haifar."

Ya kwatanta halin da kiristocin 'yan gudun hijira suka shida da irin wanda iyayen Annabi Isa Alaihissalam suka shiga lokacin da suma suka yi hijira don kaucewa kuntatawa, bayan sun haifeshi.