Fafaroma: Ku nuna ƙauna a bikin Kirismeti

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fafaroma Francis ya bukaci kiristoci su nuna kauna ga iyalai

Fafaroma Francis ya yi amfani da taron tsakiyar daren jajiberin Kirisimeti a birnin Rome, inda ya yi kira ga kiristoci da su nuna kauna ta gaskiya ga iyalai da abokai, abubuwan da yace duniya ke bukata yanzu.

A jawabin da ya yi wa dandazon mabiya darikar Katolika, Fafaroman ya nuna bukatar sauya halaye daga na alfahari da jijida kai, zuwa na kankan dakai da tausayi.

Fafaroma Francis ya aike da gaisuwar kirsimeti ta wayar tarho ga kiristocin Iraki da ke zaune a sansanin 'yan hijira a kusa da birnin Erbil na Kurdawa.

Ya kwatanta halin da kiristocin 'yan gudun hijira suka shida da irin wanda iyayen Annabi Isa Alaihissalam suka shiga lokacin da suma suka yi hijira don kaucewa kuntatawa, bayan sun haifeshi.

Dubban mabiya addinin kirista masu ziyarar ibada daga sassan duniya daban daban ne suka halarci taron ibadar na tsakiyar daren jajibarin kirsimeti, a adaddiyar mujami'ar Bethlehem inda ake gani aka haifi Annabi Isa Alaihissalam.

Masu ziyarar sun taru a wani wurin bauta mai tarihi dake yamma da kogin Jordan, domin nuna sha'awa ga wata babbar bishiya da aka kawata da launuka daban daban na tutar kasar Falasdinu.