Wasu mata na fuskantar shari'a a Saudiyya

Wata mata na tuka mota a Saudiyya. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya ita ce kasa daya tilo da mata ba sa tuka mota.

An tura Wasu mata biyu 'yan asalin kasar Saudiyya Kotu wadanda ake tsare dasu kusan wata guda, bisa keta dokar kasar na haramtawa mata tuka mota kotun hukunta laifukan ta'addanci.

Lauyoyin da ke kare su dai sun daukaka kara, an tsare daya daga cikin matan mai suna Loujain Hathloul bayan ta yi kokarin shiga Saudiya daga makofciyarta Hadaddiyar Daular larabawa.

An cafke Dayar matar Maysaa Al-amoudi wadda ta kasance 'yar jarida a Hadaddiyar daular Larabawa, wadda ta zo bakin iyakar kasar domin taimakawa Ms Hathloul.

Sai dai wasu makusantan matan sun ce ba wai ana tuhumar su ne da laifin keta dokar kasar ba, sai dan saboda ra'ayoyinsu da suke wallafawa a shafukan sada zumunta a internet.