Ebola: Saliyo ta kafa dokar hana fita

Image caption Saliyo ita ce kasar da cutar Ebola ta fi shafa a yammacin Afrika

Gwamnatin Saliyo ta sanar da dokar hana fita na tsawon kwanaki uku a arewacin kasar, yayin da ake kara kokarin dakile bazuwar cutar Ebola.

Wani kakakin gwamnati ya ce za a rufe shaguna da kasuwanni kuma babu zirga-zirgar baki dayan ababen hawa baya ga na hukumomi a kan tituna.

Haka kuma an haramta tarukan addini duk da cewa an amince cewa Kiristoci su yi shagulgulan Kirisimeti.

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa fiye da mutane dubu tara ne suka kamu da cutar a yankin Afrika ta yamma kuma har yanzu cutar na kara bazuwa.