Soyinka: 'Obasanjo makaryaci ne'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fitaccen marubuci, Wole Soyinka

Fitaccen marubucin nan na Nigeria,Farfesa Wole Soyinka ya bayyana tsohon Shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo a matsayin cikakken makaryacin da ba zai daina karya ba.

Soyinka ya maida martani ne kan abubuwan da Obasanjo ya wallafa a littafinsa mai sun 'My Watch' inda ya yi wasu kalamai marasa dadi a kan fitaccen marubucin.

A cewar Soyinka, Mr Obasanjo ya shirya karya tsagwaro a cikin littafinsa ba tare da yin nazari ba.

Marubucin ya kara da cewar Obasanjo na son kiran sunan ubangiji amma kuma a zahiri ayyukansu basa nuna cewar ya yi amanna da addinni.

A cikin litaffin na Cif Obasanjo, ya caccaki mutane da dama a Nigeria abinda ya janyo masa suka daga wurin wadanda ya aibata.